Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki Ammar Dan Yasir - Allah Ya yarda da shi - a wata tafiya dan wasu bukatunsa, sai janaba ta same shi ta hanyar jima'i ko zubar maniyyi da sha'awa, bai samu ruwa ba da zai yi wankan (janaba) ba., ya kasance bai san hukuncin taimama dan janaba ba, kadai yana da sanin hukuncinta ne dan karamin kari ne, sai ya yi ijtihadi ya yi zatan cewa kamar yadda zai shafi sashin gabban alwala daga karamin kari da turbayar dake doron kasa, to babu makawa taimama daga janaba ta kasance da game jiki da turbaya; dan kiyasi akan ruwa, sai ya jujjuya a cikin turbaya har ya game jiki ya yi sallah, lokacin da ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ambata masa hakan; dan ya ga shin akan daidai yake ko a'a? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana masa siffar tsarkaka daga karamin kari kamar fitsari, da babban kari kamar janaba: Shi ne ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa.