explain-icon

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewa mafi cancantar sharaɗin da za a cika shi ne wanda ya kasance dalili na halatta jin daɗi da mace, su ne sharuɗɗan da suke na halal ga mace ta nema a lokacin ɗaurin aure.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Wajibcin cika sharuɗɗa wanda ɗayan ma’aurata ya sa, sai dai sharaɗin da ya haramta halal, ko ya halatta haram.
  • Cika sharuɗɗan aure ya fi sauran ƙarfi, domin yana matsayin halatta farji ne.
  • Girman matsayin aure a Musulunci ta yadda ya fi kowanne sharaɗi ƙarfin cikawa.
explain-icon

Kari