Daga Abul Haura'u al-Sa'adi ya ce: Na cewa Hassan ɗan Ali - Allah Ya yarda da su -: Me ka haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -? ya ce: Na haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce". Ingantacce ne - Tirmizi da Nasa'i da Ahmad ne Suka rawaito shi
explain-icon

Explanation

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da barin abinda kake kowanto a cikinsa na maganganu da ayyuka cewa shi an hana ne koko a'a, shin shi haramun ne ko halal ne, zuwa abinda babu kokwanto a cikinsa daga abinda ka sakankance kyansa da kuma halaccinsa, domin cewa zuciya zata nutsu gare shi ta samu kwanciyar hankali, abinda kuma a cikinsa akwai kokwanto to zuciya tana kaikawo daga gareshi kuma tana raurawa.

explain-icon

Benefits from the Hadith

  • Ya wajaba akan musulmi ya gina al'amuransa akan yaƙini da barin abinda ake kokwanto a cikinsa, kuma ya zama mai basira akan Addininsa.
  • Hani daga afkawa cikin shubuhohi.
  • Idan kana son nutsuwa da hutu to kabar abinda ake kokwanto a cikinsa ka jefar da shi a gefe.
  • Rahamar Allah ga bayinSa, dan Ya umarcesu da abinda a cikinsa akwai hutun rai da zuciya, kuma ya hanesu daga abinda a cikinsa akwai raurawar zuciya da kuma ɗimuwa.