Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa shi ana dawo masa da ransa dan ya amsa sallama ga dukkan wanda ya yi masa sallama , daidai ne ya kasance a kusa yake ko a nesa; rayuwar barzahu da ƙabarbura wani al'amari ne na gaibu, babu wanda ya san haƙiƙaninsu sai Allah, Shi Mai iko ne akan dukkan komai.