Sa'ib yana bada labari cewa Yakumbonsa ta tafi dashi zuwa Manzon SAW, sai ta bawa Manzon Allah labarin cewa Xan yaruwata yana jin jiki, sai ya shafi kaina kuma yayi mun Addu'a da Albarka, sannan yayi Alwala, Sai na sha Ruwan Alwalar tasa, sannan na ta shi bayansa, sai naga Hatimin Annabta a tsakanin kafaxunsa, kamar Qwan Tattabara