Abul Ala ya Kasance Umair Bn Milhan -Allah ya yarda dashi- lokacin da Mutuwa ta zo masa, sai wani Mutum ya wuce a qarshen gida, ya ce sai naganshi a fuskar Qatada, ya ce: Kuma na kasance idan naganshi kai ka ce a fuskarsa Mai ne saboda fes xinsa da walqiyarsa da kuma haskensa kuma wancan saboda Manzon Allah SAW yashafi fuskar Qatada ne, tun daga wannan lokacin yake da wannan sheqin da walqiyar saboda Al-barkar shafawar Manzon Allah SAW da yayiwa Fuskarsa.