Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe a cikin sahabbansa yana mai huɗuba, ya kasance daga cikin abinda ya ce: Lallai cewa Allah Ya yi masa wahayi cewa ya wajaba akan mutane su yi tawali'u a tsakaninsu, hakan ta hanyar ƙanƙar da kai ga halitta da tausasa lamura, har kada wani ya yi alfahari ta hanyar da'awar girma da kafafa da ɗaukakar da zai danganta kansa ko dukiyarsa ko wanin haka akan wani, kuma kada wani ya zalinci wani, kuma kada ya yi ta'addaci akan wani.