explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wasu mutanen da zasu zauna a wani wurin zama sannan su tashi ba su anbaci Allah a cikinsa ba sai sun tashi kamar waɗanda suka taru akan mushen jaki ta ɓangaren ɗoyi da ƙazanta; hakan yayin da suka shagalta a cikin zance daga anbatan Allah, sai wurin zaman ya zama hasara a kansu a ranar alƘiyama da kuma tawaya da dana-sanin da zata lazimcesu.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa bane akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin kafin ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.
  • Hasara mai faruwa garesu a ranar alƘiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin da saɓon Allah.
  • Wannan tsoratarwar idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba (yi da wani) da annamimanci da wasunsu?!