Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya yi azimi kafin Ramadan da yini ɗaya ko yini biyu akan niyyar lissafa shi a (watan) Ramadan; domin wajabacin azimin Ramadan an rataya shi ne da ganin jinjirin wata, babu buƙatuwa ga ɗorawa kai, sai dai wani wanda ya kasance yana yin wani azimin da ya sabayi kamar azimin yini da fashin yini (irin na annabi Dawud), ko ranar litinin ko alhamis sai ya yi daidai da shi to ya azimce shi; wannan bai zamo daga tarbar Ramadan a wani abu ba, an riskar da hakan abinda ya kasance azimi ne na wajibi kamar ramuwa da bakance.