Umaimah 'yar Ruƙaiƙah - Allah Ya yarda da ita -: Cewa ita ta zo wurin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tare da ita akwai wasu mata daga matan Madina, zasu yi masa caffa (mubaya’a) akan ba zasu yi wa Allah shirka da wani abu ba, kuma ba zasu yi sata ba, ba zasu yi zina ba, ba zasu zo wa ƙirƙirarriyar ƙaryar ba da zasu aika tsakanin hannayensu da ƙafafuwansu ba, kuma ba zasu saɓa masa a wani aikin alheri ba, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: A cikin abinda zaku iya, kuma kuke da iko, Muka ce: Allah da manzonSa ne mafi jin ƙai da mu, ka zo mu yi maka caffa (mubaya’a) ya manzon Allah da gaisawa hannu da hannu kamar yadda maza suke yi maka, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Lallai ni bana gaisawa da mata hannu da hannu, kawai maganata da mubaya'ata ga mata ɗari kamar maganata ce ga mace ɗaya.