explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi sallar nafila raka'a huɗu kafin sallar Azahar, da raka'o'i huɗu a bayanta albishir, kuma ya dawwama ya kiyaye akansu (cewa) Allah Zai haramta wuta gare shi .

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • An so kiyayewa akan raka'o'i huɗu kafin Azahar da (raka'o'i) huɗu a bayanta.
  • Salloli ratibai kafin sallah - wato kafin farillah -; suna da hikimomi, daga cikinsu: Yi wa zuciyar mai sallah tanadi ga ibada kafin shiga cikin farilla, amma na bayan sallah daga cikin hikimominsu akwai gyara kuskure a farillai.
  • Akwai fa'idoji da yawa a (salloli) ratibai, na ƙarin kyawawan ayyuka, da kankare munanan ayyuka, da ɗaga darajoji.
  • Ka'idojin Ahlus Sunnah a cikin hadisan alkawari irin wannan hadisin: Ita ce a ɗauki (hadisan) akan mutuwa akan tauhidi, kuma cewa abin nufi rashin dawwama a cikin wuta; domin mai aikata zunubai cikin masu tauhidi ya cancanci uƙuba sai dai ba zai dawwama a cikin wuta ba in an yi masa uƙuba.