Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga zagin sahabbai, musamman ma marigaya na farko daga muhajirai da mutanen Madina; kuma ya bada labarin cewa shi da wani daga mutane zai ciyar da kwatankwacin dutsen Uhudu na zinari ladansa ba zai kai ladan ciyarwar wani daga sahabbai ba mudu na abinci ko rabinsa ba - mudu shi ne cikin tafuka biyu na mutum matsakaicin halitta -; hakan dan ƙarin ikhlasinsu, da gaskiyar niyyarsu, da rigayar ciyarwarsu da yaƙinsu kafin buɗe Makka inda tsananin buƙatuwa gare shi take.