explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Mala'iku ba sa tafiya a ayari a atare dasu akwai kare, ko ƙararraar da ake ratayawa a wuyan dabbobi, sai ya fara kara idan an dabbar na tafiya.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Hani daga daukar karnuka da tafiya da su, in banda karen farauta ko na gadi.
  • Mala'iku wadanda ba sa tafiya da (karnuka da kararrawa) su ne Mala'ikun rahama, amma masu rubuta ayyukan bayi to su ba sa rabuwa da bayi a zamansu da tafiye-tafiyensu.
  • Hani daga ƙararrawa; Domin cewa ita garayace daga garayoyin shaidan, kuma a cikinta akwai kamanceceniya da gangar kiristoci.
  • Ya wajaba akan musulmi ya yi kwadayi akan nisanta da dukkanin abinda sha'aninsa shi ne nisantar da mala'iku daga gare shi.