explain-icon

Explanation

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa huɗuba, daga cikin abinda ya yi musu wasicci da shi cewa kada tsoro da kwarjinin mutane da kuma ƙarfinsu ya hana musulmi faɗin gaskiya ko umarni da ita idan ya ganta ko ya santa.

explain-icon

Benefits from the Hadith

  • Kwaɗaitarwa akan bayyanar da gaskiya da kuma rashin ɓoyeta dan jin tsoron mutane.
  • Faɗin gaskiya ba ya nufin rashin lazimtar ladabi ta hanyar faɗinta da kuma hikima da kyakkyawan wa'azi a cikinta.
  • Wajabcin inkarin munkari, da kuma gabatar da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - akan mas'lahohin mutane waɗanda sukaci karo da ita.