Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku cika sawun gaba, sannan wanda ke biye da shi, abin da aka samu tawaya daga gare shi to ya zama a cikin sawun ƙarshe ne». Ingantacce ne - Abu Dawud da Nasa'i ne suka ruwaito shi