Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai daga cikin mutane wanda gashin kansa a cukurkuɗe yake, ya yi ƙura, ba ya shafa masa mai, kuma ba ya yawan wanke shi, ba shi da wata daraja a wurin mutane dan haka suke ture shi a bakin ƙofofinsu, suna korarsa dan wulaƙanta shi; saidai cewa shi da ace zai yi rantsuwa akan faruwar wani abu da Allah Ya farar da abun, dan girmama shi da amsa roƙonsa, da kuma kiyaye shi daga warware rantsuwarsa, hakan saboda falalarsa da matsayinsa a wurin Allah.