explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitarwa Abu Zarr al-Gifari - Allah Ya yarda da shi - cewa idan zai dafa romo to ya yawaita ruwansa, ya bibiyi maƙotansa da shi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa akan kyakkyawar mu'amala tare da maƙota.
  • An so yin kyauta tsakanin maƙota; domin hakan yana gadar da soyayya kuma yana ƙara ƙauna, wannan kyautar tana ƙarfafuwa idan abincin yana da ƙanshi, kuma an san buƙatuwar maƙoci (gare shi).
  • Kwaɗaitarwa akan bada abin alheri da abinda ya sawwaƙa daga gare shi koda kaɗan ne, da shigar da farin ciki ga musulmai.