explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake da sama da mace (ɗaya), bai yi adalci tsakanin matansa gwargwadon iko ba na daidaitawa tsakaninsu a ciyarwa da wurin zama da abin sawa da wurin kwana, cewa uƙubarsa a ranar alƙiyama ta kasance ne rabin jikinsa a karkace, kuma karkacewarsa uƙuba ce gare shi akan zalincinsa, kamar yadda ya karkata a cikin mu'amalarsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Wajabcin raban kwana akan namiji tsakanin matansa biyu ko matansa da yawa, kuma karkata zuwa ga ɗayansu ya bar sauran yana haramta, a abinda yake da iko akansa na ciyarwa, da wurin zama, da kyakkyawar tarba, da makamancin hakan.
  • Daidaito a rabon kwana da makamancin haka, a abinda mutum yake iya mallakarsa, amma a abinda ba ya iya mallakinsa kamar soyayya da karkata ta zuciya to cewa shi ba ya shiga cikin hadisin, kuma shi ne abin nufi a cikin faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Ba zaku iya adalci a tsakanin mata ba koda kun yi kwaɗayi} [al-Nisa'i: 129].
  • Sakayya tana kasancewa ne daga jinsin aiki, cewa mutum a lokacin da ya karkata a duniya daga wata mace zuwa wata, zai zo a ranar alƙiyama ɗaya daga tsagin jikinsa ya karkace daga ɗayan.
  • Girmama haƙƙoƙin bayi, kuma cewa ba'a kau da kai a kansu; domin cewa su ababen ginawa ne akan ƙwauro da sakayya.
  • An so taƙaituwa akan mace ɗaya idan namiji ya ji tsoron kada ya yi adalci tsakanin matansa; dan kada ya faɗa a cikin gazawa a cikin Addini; Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba to (ku auri mace) ɗaya} [al-Nisa'i: 3].