explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana alamar shigar watan Ramadan da kuma fitarsa, sai ya ce: Idan kun ga injirin watan Ramadan to ku azimce shi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwanaki talatin na watan Sha'aban, idan kun ga jinjirin watan Shawwal to ku ajiye azumi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwana talatin ga watan Ramadan.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Dogara a tabbatar da shigar wata akan gani ne ba akan lissafi ba.
  • Ibunl Munzir ya cirato ijma'i akan cewa azimi ba ya wajaba idan shigar watan Ramadan ya kasance da lissafi ne kawai ba ganin (wata) ba.
  • Wajabcin cika Sha'aban kwana talatin idan girgije ko makancinsa ya tsare ganin jinjirin watan Ramadan.
  • Watan sama ba ya kasancewa sai kwana ashirin da tara, ko kwanaki talatin.
  • Wajabcin cika Ramadan kwanaki talatin idan girgije ko waninsa ya tsare (ganin) jinjirin watan Shawwal.
  • Wanda yake a wurin da babu wanda yake bibiyar al'amarin musulmai a sha'anin azimi, ko akwai wanda bai kula da hakan ba to yana kamata ya kiyaye hakan ya bibiye shi da wanda hakan yake tabbata a wurinsa da ganin kansa ko da ganin wanda ya aminta da shi; sai ya yi azimi da hakan kuma yasha ruwa.
explain-icon

Kari