Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Abubakar da Umar: "Waɗannan biyun sune shugabannin dattijan 'yan aljanna daga na farko dana ƙarshe sai dai Annabwa da Manzanni".
Ingantacce ne - Tirmizi ne ya ruwaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Abubakar Siddiƙ da Umar Faruƙ - Allah Ya yarda da su - sune mafifitan mutane bayan Annabawa, kuma mafifitan waɗanda suka shiga aljanna bayan Annabwa da Manzanni.
Daga Cikin Fa idodin Hadisin
Abubakar da Umar - Allah Ya yarda da su - sune mafifitan mutane bayan Annabawa da Manzanni.
A aljanna babu tsoho, kai, wanda zai shigeta ɗan shekara talatin da uku ne, abin nufi cewa sune shugabannin wanda ya mutu yana dattijo a duniya, ko kuma hakan izina ne na abinda suke akansa a duniya a lokacin wannan hadisin.