explain-icon

Explanation

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar masu yin sallah kan su daidaita sahunsu, kuma kada sashinsu ya gabata akan sashi kada kuma ya jinkirta, kuma daidaita sahu yana daga cikar sallah , kuma karkace sahu ɓaci ne da tawaya a sallah.

explain-icon

Benefits from the Hadith

  • Halaccin kula da dukkan abinda yake cika sallah kuma yake nisantar da ita daga tawaya.
  • Hikimar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a koyarwa, ta inda ya haɗa hukunci tare da dalilinsa; dan bayyanar da hikimar shar'amtawa, da nishaɗantar da rayuka akan kamantawa.