Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya zo wa matarsa ta duburarta tsinanne ne".
Hasan ne - Abu Dawud da Nasa'i cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga miji ya zo wa matarsa ta duburarta; cewa shi tsinanne ne abin korewa daga rahamar Allah, kuma shi babban laifi ne cikin manyan laifuka.
لە سوودەکانی فەرموودەکە
Haramcin zakkewa mata ta duburarsu.
Jin daɗi daga mata a koma bayan duburarta na jikinta ya halatta.
Musulmi yana zakkewa mace ne ta farjinta kamar yadda Allah Ya umarce shi; amma ta dubura to a cikin hakan akwai ɓata ɗabi'a, da tozarta zuriya, da saɓawa abinda nagartattun ɗabi'u suke a kansa, da kuma cutuka masu kaiwa ga ma'auratan.