Daga Dan Abbas -Allah ya yarda dasu-ya ga wani mutum ya firgita yayin da yaji wani hadisi game da Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- game da sifofin Allah-don nuna rashin yardarsa da haka- sai yace: Meye banbancin wadannan?zuciyarsu na yin taushi in suka ji ayoyi bayyanannu,su kuma rikice in suka ji ayoyi masu rikitarwa". Ingantacce ne - Ibnu Abi Asim ya rawaito shi - Abdurrazak Ya Rawaito shi