explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ɓarawo ana yanke hannunsa saboda satar rubu'in dinari na zinare, da abinda ya ƙaru a kan hakan, kuma ya yi daidai da abinda ƙimarsa ta yi daidai da ƙimar 1.06 Gram na zinari.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Sata tana daga cikin manyan zunubai.
  • Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya iyakance uƙubar ɓarawo, ita ce yanke hannunsa; kamar yadda yake a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Barawo da ɓarauniya to ku yanke hannayensu} [al-Ma'ida: 38], kuma sunnah ta bayyana sharuɗɗan wannan yankewar.
  • Abin nufi da hannu a cikin hadisin shi ne yanke tafi daga gaɓarsa tsakaninsa da tsakanin damtse.
  • Daga hikima a cikin yanke hannun ɓarawo, (akwai) kiyaye dukiyoyin mutane, da tsawatar da waninsa (ɓarawon) cikin masu ta'addanci.
  • Dinari awo ne na zinare, kuma ya yi daidai a yanzu da (4.25 KG) awon 24; to ɗaya bisa huɗu na dinari ya yi daidai da Gram da wani abu.