Wannan hadisi yana nuni da lokacin da yafi a yi kowacce daga cikin salloli biyar,ka ga sallar Azahar:ana yin tane lokacin da rana ta karkata daga tsakkiya,shi ne lokacin zawali, shi ne farkon lokacinta.La'a sar kuma: ana yinta lokacin da rana take fara fat, ba wani fatsi-fatsi da ya gauraya da ita,yadda ake gane lokacinta shi ne tsawon komai ya lunka, Magariba kuma ana yinta ne lokacin faduwar rana da sanda ta buya. Issha'i kuma sai a kula da yanayin mutane in sun zo da wuri a farkon lokacinta,shi ne lokacin buyan jan shafaki to sai a yi ta, in kuma basu zo ba to sai a jinkirta ta har wajen tsakkiyar dare na farko, don shi ne lokacinta da ya fi ba don takurawa ba. amma Asuba shi ne farkon lokacin da haske ya fara dan bullowa