Annabi tsira da aminci su tabbata agareshi yana yiwa Al'umarsa bushara da cewa hakika Allah maitsarki da daukaka yana kebantarsu da Alamar fifiko da daukaka ranar Alkiyama,a tsakanin Al'umai,ta yarda za'a kirawosu sai su zo agaban Halittu Fuskokinsu daHannayensu da Kafafuwansu suna kyalkyali na haske, wancananka gurbine daga guraben wannan Ibada maigirma,itace Alwala wacce suka dinga maimaitata abisa wannan Gabobi masu Alfarma don neman yardar Allah, da kuma neman ladansa, sai sakamakonsu ya kasance wannan girmamawar maigirma kebantacciya.Sannan Abu Huraira Allah ya yarda dashi yake cewa: "Wanda ya sami ikon tsawaita wannan Fari to ya aikata" domin cewashi duk sanda ya tsawaita bigiran wankewa daga Gaba Fari da kyalkyali zai karu, domin cewa adon Hasken yana kaiwa inda Ruwan Alwala ya kai, sai dai abin shar'antawa kawai wanke Hannaye biyu acikin Alwala ya zama zuwa gwiwar Hannaye biyu ya shigar da gwiwar da farawa da Dantse da wanke wani yanki daga gareshi, da kuma wanke Diga Digai biyu izuwa Idon sawaye biyu ya shigar da Idon sawayen biyu da farawa da kauri, kuma ba'a shara'anta wanke Dantse da kauri acikin Alwala ba