Dan Umar -Allah ya yarda dasu- wata rana yazo gidan 'yar'uwarsa Hafsa,Matar Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-sai ya hau saman gidanta, sai ya gano Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- yana biyan bukatarsa ya fuskanci Sham,ya kuma juyawa Alkibla baya.Dan Umar Allah ya yarda da shi- ya fadi haka don yin raddi ga wadanda suka ce:Annabi baya fuskantar Baitalmakdis lokacin biyan bukata,daga nan kuma sai Mawallafin ya zo da ruwaya ta biyu wacce take cewa: yana mai fuskantar Baitalmakdis.