explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da wanke kwarya sau bakwai idan kare ya shigar da harshensa a cikinta, na farko daga cikinsu a haɗa da turbaya sai ruwa ya biyo bayanta, sai cikakkiyar tsafta ta tabbata daga najasarsa da kuma cutarsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Yawun kare najasa ne najasa mai kauri.
  • Lallagin kare a cikin kwarya yana maida ita mai najasa, kuma yana najasantar da ruwan dake cikinta.
  • Tsarkakewa da turbaya da maimaitawa sau bakwai ya kebanci tsarkakewa ne daga lallaginsa banda fitsarinsa da bayan gidansa, da ragowar abinda kare ya bata shi .
  • Yadda wanke kwarya da turbaya: A sanya ruwa a cikin kwarya sai a zuba turbaya (kasa) a ciki, sannan a wanke kwarya da wannan cuɗaɗɗen.
  • Zahirin Hadisin mai gamewa ne a dukkanin karnuka, har karnukan da shari’a ta bada iznin a dauke su, misalin karnukan farauta da na gadi da na kiwo.
  • Sabulu da makilin ba sa tsayawa a matsayin turbaya; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nassanta turbaya ne.