explain-icon

Explanation

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yawaita tinanin mutuwa, da tinaninta ne mutum yake tuna lahira, kuma soyayyarsa ga duniya ta rushe a cikin zuciyarsa, musammanma dai abubuwan da aka haramta.

explain-icon

Benefits from the Hadith

  • Mutuwa tana yanke jin daɗin duniya, sai dai a haƙƙin mumini tana dago shi zuwa jin daɗin lahira da jin daɗin aljanna da abinda yake faruwa a cikinta na alheri mai girma.
  • Tina mutuwa da abinda ke bayanta yana daga sabubban tuba da barin laifi da kuma tanadi dan lahira.