Daga Abdurrahman Dan samra yana cewa cewa Annabi ya ce masa: "Ya kai Abdurraahman Dan Samra, kada ka kuskura ka nemi Mulki, cewa in aka baka shi sabida ka nema sai a barka da kanaka, kuma in aka baka bakai ka nema ba sai Allah ya taimakeka akansa, kuma idan kayi rantsuwa akan wani abu sai kaga wani mafi alkairi daga rantsuwar, to kayi kaffarar rantsuwarka, kuma kayi abinda yafi Alkairin" Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi