Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa zukatan 'ya'yan Adam dukkansu suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun (Ubangijin) shi ne al-Rahman kamar zuciya ɗaya; Yana juya ta yadda Ya so; idan Ya so Ya tsayar da ita akan gaskiya, idan kuma Ya ga dama ya karkatar da ita daga gaskiya, kuma jujjuyawarSa a cikin dukkannin zukata kamar tasarrufi ne a abu ɗaya, wani sha'ani ba ya shagaltar da Shi - tsarki ya tabbatar maSa - daga wani sha'anin, sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi adu'a sai ya ce: Ya Allah ya Mai jujjuya zukata wani lokaci zuwa ga ɗa'a, wani lokaci kuma zuwa saɓo, wani lokaci kuma zuwa tinawa wani lokaci kuma zuwa rafkana, ka juyar da zukatanmu akan biyayyarKa.