explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana falalar addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama, kuma cewa ba'a dawo da ita kuma ta cancanci amsawa, to ku roƙi Allah a cikinsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar wannan lokacin dan yin addu'a.
  • Idan mai yin addu'a ya siffantu da ladubban addu'a, kuma ya nufi gurarenta da lokutanta masu falala, kuma ya nisanta daga saɓon Allah, Ya tsare kansa daga afkawa a cikin shubuhohi da kokwanto, kuma ya kyautatawa Allah zato: To shi ya cancanci a amsa masa da izinin Allah.
  • Al-Manawi ya ce game da amsa addu'a: Wato: Bayan tara sharuɗɗan addu'a da rukunanta da ladubbanta, idan wani abu ya saɓa daga garesu to kada ya zargi kowa sai kansa.
  • Amsa addu'a: Kodai a gaggauto masa da abinda ya roka, ko a kawar masa da sharri kwatankwacin sa, ko a ajiye masa ita a lahira; hakan gwargwadan hikimar Allah da rahamarSa.