Mai yin sallan a gaban Ubangijinsa yake yana ganawa da shi, idan wani ya wuce ta gabasnsa to ya yanke wannan ganawar kuma ya rikita masa sallarsa,don haka zunubin wanda ya janyo matsala cikin sallar mai salla ya zama babba Don haka shari'a ta bayyana cewar da ya san abin da ke kansa na zunubi a dalilin waucewarsa ta gaban masallaci,da ya gwammace ya tsaya cak har lokaci mai tsawo da a ce ya wuce ta gaban mai sallah, gujewa hakan ya zama tilas