An samu wata baiwa a lokacin Manzon Allah SAW an rotse mata kai a tsakanin duwatsu biyu, nbata karasa Mutuwa, sai suka tambayeta ta hanyar kirga mata sunaye wadanda ake sa ran sunyi mata abun, har suka zo kan sunan wani Bayahude sai ta yi nuni dakanta cewa E, wannan shi ne wanda ya rotse mata kan, sai ya zamanto abun tuhuma da kasha ta, sai suka kama shi suka titsiye shi har yayi Ikirarin da Kashe ta, saboda wani adon Azurfa a jikinta, Sai Annabi SAW yayi Umarni a saka masa da kwatankwacin, sai aka roste kansa shi ma a tsakanin duwatsu biyu.