Daga Abi huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda yayi Wankan Gawa to yayi Wanka shi ma, kuma duk wanda ya xauketa to ya sake Alwala"
Ingantacce ne - Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi