Ranar idin karamar sallah da ranar idin babbar sallah na daga cikin ranaku masu falala, wadanda alamomin musulunci ke bayyana a cikinsu`yan`uwantakar musulmi tana bayyana a fili ta hanyar haduwar su waje daya da tattaruwar su a sahu-sahu, dukkan mutanen gari suna tattaruwa a waje guda don bayyanar da hadin kan su, da haduwar zukatan su, da haduwar kalmar su bisa taimakon addinin musulunci, da daukaka kalmar Allah tare da tsaida ambaton Allah da bayyanar da alamominsa. saboda haka ne annabi mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi yayi umarni da a fitowar dukkan mata, harma da dukkan `yan matan da aka suturce su cikin gidajen su fitowar tana kansu, da mata masu jinin haila, saidai zasu zauna ne a nesa da masu sallah, domin su halarci alheri da addu`ar musulmai sai su samu alheran wannan taro, su kuma samu albarka sa, da samun rahamar Allah da yardar sa don rahamar ta kasance da samun karbuwa ta zamo mafi kusa garesu. sallar idi guda biyu farilla ce ta kifaya.