Daga Abdullahi Dan Umar -Allah ya yarda da su- ya ce: "Annabi ya kasance -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- da Abubakar da Umar sunayin Sallar Idi kafin Huduba" Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
explain-icon

Bayani

Yakasance yana daga Al'adar Annabi da Halifofinsa, cewa sunayin Sallar Idi da Mutane, a karamar sallah da Babba, kuma suyi Huduba kuma su fara Sallah kafin Huduba, kuma hakan yaci gaba da faruwa har zuwan Marwan shi ne yayi Huduba kafin Sallah