An rawaito daga Yazid Bn Sharik Bn Tarik, ya ce: naga Ali -Allah ya yarda da shi- akan Minbari yana huduba sai naji shi yana cewa: Aa Wallahi bamu da wani littafi da muke karantawa sai Littafin Allah da abin da yake cikin Takarda sai ya budeta sai gashi a cikinta akwai: Hakoran Rakumi, da wasu abubuwa na Mikuna, kuma a cikinta Manzon Allah ya ce: "Madina Harami ce tsakanin Dutsen Eir har zuwa Dutsen Sauru, sabda haka duk wanda ya farar da wata Barna a cikinta, ko ya boye wanda ya farar da ita, to La'antar Allah ta tabbata a gare shi da Mala'ikun Allah da Mutane baki daya, Kuma Allah ba zai karbi komai daga gare shi ba na tuba ko kuma na fansa" Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi