explain-icon

Explanation

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iyakance akan rage gashin bakin namiji, da yanke farcen hannaye da ƙafafuwa, da cire gashin hammata, da aske gashin mara, cewa kada a barsu sama da kwanaki arba'in.

explain-icon

Benefits from the Hadith

  • Shaukani ya ce: Abin aka fi so shi ne a iyakance kwana arba'in waɗanda manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iyakance su dan haka ba ya halatta a ƙetaresu, wanda ya bar askewar da makamncinsa bayan tsawo har zuwa ƙarshen waccan lokacin na kwanaki arba’in to ba za'a ƙirga shi cikin wanda ya saɓawa sunnah ba.
  • Ibnu Hubaira ya ce: Wannan hadisin shi ne matuƙa a jinkirta hakan, abinda ya fi a yi riƙo da ƙasa da wannan matuƙar.
  • Kulawar musulunci da tsafta da tsarkaka da kuma ado.
  • Rage gashin baki, shi ne a rage wasu daga gashin da ya tsiro akan leɓe na sama.
  • Cire gashin hammata, yana kasancewa ne da kawar da gashin da yake tsirowa da shi, shi ne gurin da yake kasancewa ƙasan mararrabar zira'i da kafaɗa.
  • Aske gashin mara, shi ne gashi mai kaushi wanda ya tsiro a gefen gaba daga namiji da mace.