Wannan Hadisin yana nuna cewa a cikin Shuwagabannin Musulmi akwai Nagari akwai kuma wadan da suke da Fasikanci da karancin Addini, kuma duk da hakan bai halarta ayi musu tawaye ba matukar dai suna kulawa da Sallah da abubuwan Musulunci, kuma ya Karfafa tsaida Sallah