Annabi ya tsai karwatar da Sahabbansa daga zama a kan Hanyoyi, sai suka ce: babu makawa kuwa ga barisa, sai ya ce: idan kunki babu makawa zasu zauna to ya wajaba akanku ku bawa Hanya hakkinta, sai ya basu labari da shi: to su runtse Idanuwansa ga barin kallon Mata da suke wucewa ta gabansu kuma su kaucewa cutar da Masu wucewa da magana ko da aiki, kuma su rika mayar da Sallama ga duk wanda ya wuce su, kuma su rika umarni da kyakkyawan Aiki da hani da Mummuna idan suka ganshi a gaban su wanda ya wajaba ayi Inkarinsa.