An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu" kuma na rantse da wanda Ran Abuhuraira ya ke a Hannunsa ba don Jihadi a tafarkin Allah ba da kuma Hajji, da kuma biyayyar Mahaifiyata ba, da nai kwadayin na Mutu ina Bawa Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi