Musulunci ya zo, kuma ka gusarwa Mutane dukkan kazantar Jahiyya, Musamman ma ga Mata, domin suna munana Mu'amala ga Matan kuma suna Zaluntarta, Sai Musulunci ya kwato mata hakkinta, to a cikin wannan Hadisin wata Mata ta zo tana neman fatawar Annabi cewa Mijin Diyarta ya Mutu, kuma zata yi masa Iddakuma Mai Idda bata Kwalliya, saidai kuma tana fama da ciwon Ido, shin anyi mata rangwame da ta yi amfani da Kwalli ne? sai Annabi ya ce Mata AA kuma yana mai maimaita mata hakan, sannan ya karanta mata ganin tsawon muddar Iddar tata, wanda Mace zata yi Idda ne fa don Alfarmar Mijinta tsawon wata hudu da kwana goma, yanzu ba zata iya jurewa ba a wanna Dan lokacin kadan wanda ba shi da wani tsawo? kuma Mata sun kasance a Jahiliyya, suna shiga Idda ne cikin Dan wani karamin Daki kamaer wani ramin kura, kuma su daina kwalliya, da saka turare, haka ma yin amfani da ruwa, da kuma cudanya da Mutane, sai Mace tayi cidin cidin da Dauda da kazanta na rashin wanka, kuma ba ita babu Mutane, shekara guda cur, to idan ta gama gama iddar sai a bata kashin Rakumi tayi jifa da shi, wannan shi yake nuna cewa duk wannan wahalar da ta shiga babu wani abu na kimantawa da ta yi na wannan abu da tayi don Mijinta sai wannan wulakantaccen abun (KashinRakumi) sa i Musulunci ya zo ya canza Mata waccan wahala da wata Ni'ama, da kuma wancan tsananin, kuma Sannan yaya ba zata iya hakuri ba da kwallin Idonta, to don haka babu Rangwame a gareta, don kada hakan ya zama tsani izuwa bude kofar Ado ga Mai Takaba.