Abu Amr Dan Hafs ya nisanta daga Matarsa ta hanyar saki Matarsa Fadima Yar Kais, kuma wannan shi ne karshen Saki ne a gare ta, kuma duk wacce aka saka saki uku batada ciyarwa akan Mijinta, sai dai shi ya aika mata da Acca, sai ta zaci cewa ciyar da ita Wajibi ne akansa Matukar dai tana cikin Idda, sai ta raina Acca din kuma taji bata so,sai ya rantse cewa batada komai akansa, sai ta kai kararsa zuwa ga Annabi, sai ya bata labari cewa batada komai akansa kuma bata da wurin zama, kuma sai aka Umarce ta cewa tayi Idda a cikin gidan Ummu Shuraik, kuma yayin da aka gayawa Annabi cewa Ummu Shuraik Sahabbai Maza suna yawan zuwa gidanta, sai ya Umarce ta tayi Idda a gidan Dan Maktoom kasancewarsa Makaho ne, kuma bazai ganta ba koda ta cire kayanta kuma ya ce ta gaya masa idan ta gama Idda. Yayin da ta gama Idda sai Mua'wiya ya nemi Aurenta, da kuma Abu Jahm, sai ta nemi shawarar Annabi a cikin haka. sabida cewa Nasiha wajibi ce -Musamman ga wanda aka nemi shawararsa- to cewa bai mata shawara ba da ko daya; sabida Abu Jahm akwai shi da Tsanani ga Mata kuma shi Mu'awiya talaka ne bashi da kudi, kuma sai ya Umarce ta da ta Auri Usama, sai taji bata sonsa kasancewar sa Bararren Bawa ne, kuma sai dai ita tabi Umarnin Annabi, sai ta karbe shi, kuma tayi farin ciki da hakan, kuma Allah ya sanya Alkairi mai yawa a ciki.