Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya je wani yaki tare da sahabbansa yawancinsu a kasa suke,sai suka gaji har suka nannada yanki a kafafuwansu, duk da dai ba'a yi yakin ba, musulmi ne suka tsorata abokan gabarsu, to a wannan hadisin abokan gab a ba'a bangaren Alkibla suke ba,saboda gidajensu suna gabas da Madina,sai Annabi ya kasa su kashi biyu,wasu suka yi sahu tare da shi,wasu kuma suka fuskanci abokan gaba wadanda masu salla suka juya musu baya,sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sallaci raka'a daya tare da sahun farko,sai suka ciko raka'a daya suka yi sallama,sannan suka je suka fuskanci abokan gaba,shi kuma ya tsaya a tsaye, har wadancan masu fuskantar abokan gaba suka zo, ya sallaci raka'ar da ta rage tare da su, sai yayi zamansa suka mike suka ciko raka'a daya,sannan yayi sallama suma suka yi.Jama'ar farko sun dace da samun kabbarar harama tare da liman,ita kuma ta biyu ta dace da samun sallama tare da liman,kuma abokan gaba basu sami dama ba,sahabbai kuma sun samu daidaito wajen samun falalar jam'in.