Yayin da Annabi -tsira da amincin Allah- ya fita izuwa Zulhulaifa " Mikatin Mutanen Madina" don yin Hajjinsa ta bankwana, yayi bankwana da Dakin Allah yayi bankwana da mutane, yayi bankwana da Aikin hajjin, kuma ya shaidar da cewa ya isar da sakon Allah zuwa ga mutane, sai ya daura haramin yin umara da hajji, sai yayi kirani, Kirani shi ne Tamattu'i, sai mutane suka yi tamattu'i tare da Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi- wasu suka yi haramar yin umra da hajji gaba daya, wasu kuma suka yi haramar yin umara, tare da niyyar yin hajji bayan sun gama umra, wasu kuma suka yi niyyar yin hajji kadai,Annabi -tsira da amincin Allah ya basu zabi tsakanin abu ukun, Annabi tsira da aminci da wasu daga sahabbai suka taho da hadayarsu daga Zulhulaifa, wasu kuma basu taho da ita ba, yayin da suka kusa da Makka sai Annabi tsira da amincin Allah ya kwadaitar da wadanda suke ifradi da masu kirani amma basu taho da hadaya ba su mayar da niyyarsu ta yin umara, bayan sunyi dawafi da saayi sai yace su yi saisaye, su warware umararsu sannan suyi harramar hajji kuma suyi hadaya, saboda yin umara da hajji a tafiya daya, wanda kuma bashi da hadaya, to yayi azumi goma, uku a can bakwai kuma in ya koma garinsu.Lokacin da Annabi tsira da amincin Allah yazo Makka sai ya sumbaci Rukni, yayi dawafi bakwai, yayi uku da sauri kasancewar sune na farko bayan zuwansa, yayi hudu a hankali, sannan yayi salla raka'a biyu a Makamu Ibrahim, sannan yayi Safa da Marwa sau bakwai, yana yin sassarfa a tsakanin alamomi biyu, yayi tafiya a inda ba nan ba, kuma bai kwance haraminsa ba har sai da ya gama hajji, ya soke hadayarsa ranar sokewa, bayan ya gama hajjinsa ya jefi Jamrat Al'akba, ya soke hadayarsa, ya aske kansa. Wannan shine tahalluli na farko, sai yayi dawafin ifadwa, sannan ya halarta komai, harma da kusantar iyali, duk sahabban da suka zo da hadaya suma suka yi haka.