Wannan Hadisin yana nuna cewa Manzon Allah SAW yayi hajji akan Taguwa wacce akanta akwai Tsohon Sirdi da Shinfixar da bara wuce Dirhami huxu ba, ko ma qasa da wannan kuxin, sannan ya ce: Wannan Hajjin banyi ta ba don saboda mutane su ganni ko su ji ni, nayi ta ne kaxai dominka, kuma saboda ka yarda da ni