explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa kan mu faɗi kuma mu maimaita kalamr Tauhidi "La'ilaha illallahu" a wurin wanda fizgar mutuwa ta zo masa har sai ya faɗeta, dan ta zama ƙarshen maganarsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • An so yi wa wanda mutuwa ta halarto masa talƙini.
  • An karhanta yawaita yin talƙini ga wanda mutuwa ta halarto masa, da kuma nacewa a kansa idan ya karɓi talƙinin, ko an fahimci hakan daga gare shi; dan kada ya takura masa sai ya furta abin da bai dace ba.
  • Nawawi ya ce: Idan ya faɗeta sau ɗaya to kada ya maimaita masa saidai idan ya yi wata maganar daban a bayansa, sai asake bijiro masa da ita dan ta zama ita ce ƙarshen zancensa.
  • Hadisin ya ƙunshi halartar wurin da wanda mutuwa ta halarto masa dan tinatar da shi da kuma yi debe masa kewa da rintse idanuwansa da kuma tsayuwa da haƙƙoƙinsa.
  • Rashin halaccin yin talƙini bayan mutuwa da wurin ƙabari bayan an binne; saboda rashin aikata hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.