explain-icon

Bayani

Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labari, cewa daga abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tabbatar da shi a cikin sunnarsa, shi ne mai kiran sallah ya ce a cikin kiran sallar Asuba kadai, bayan faɗinsa: (Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira)), ya ce: (Assalatu khairun minan naum (sallah tafi bacci alheri)).

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Faɗinsa: (Yana daga sunnah): Yana nufin sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, to shi yana da hukuncin Raf'u, wato wanda aka danganta shi zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • An so mai kiran sallah a cikin kiran sallar Asuba ya ce bayan ya faɗi: Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira): Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri), sau biyu; domin sallar Asuba a lokacin da mutane suke bacci ne a cikinsa, zasu tashi daga bacci zuwa sallah, sai aka keɓanci sallar Asuba da hakan banda sauran sallolin.