Kuma wannan Hadisin riwaya biyu aka samu, Kuma abunda ya ke a fili na siyakin, cewa abubuwa biyu ne suka faru ba abu daya ba, Na farko: ceawa wani Mutum yazo wajen Annabi Tsira da Amincin Allah Su tabbata a gare shi to sai ya bada labarin cewa Mahaifiyarsa ta Mutu kuma ana binta bashin Azumin ta yi Bakancensa shin zai iya rama mata? Riwaya ta biyu: Cewa wata Mata ta zo wajen Mazon Allah -Tsira da Aminc in Allah Su tabbata a gare shi -ceawa wata Mata ta zo wajen Annabi -Tsira da Amincin Allah Su tabbata a gare shi- to sai ya bada labarin cewa Mahaifiyarta ta Mutu kuma ana binta bashin Azumin ta yi Bakancensa shin zai iya rama mata? to duka kuma ya basu fatawa da raa Azumin, sannan ya buga musu Misali da abun da zai kusanta musu da fahimtar abunda yake muwa ga Iyayensu nufi kuma ya kara musu bayani Kuma: shi ne cewwa lallai wannan Azumin Bashi ne na Allah akan Iyayen su, to idan bashin Mutum za'a biya to bashin Allah shi ne mafi cancanta da a biya.